Ganawa a tsakanin shugabannin Sin da Amurka tana da babbar ma'ana ga kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin manyan kasashe
Game da ganawa a tsakanin shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama a jihar California dake kasar Amurka a ranar 7 zuwa 8 ga watan Yuni, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a ranar 21 ga wata a nan birnin Beijing cewa, ganawar tana da babbar ma'ana ga kasashen biyu wajen kara yin mu'amala, fahimtar juna, zurfafa hadin gwiwa, daidaita matsaloli, da kuma sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka a tsakaninsu da kuma kafa sabuwar dangantaka a tsakaninsu.
A cikin sanarwar da fadar shugaban kasar Amurka wato White House ta bayar, an ce, shugabannin kasashen biyu za su waiwayi nasarorin da kasashen biyu suka samu da kalubalen da suka fuskanta a shekaru 4 da suka gabata, kana za su tattauna yadda za a kara yin hadin gwiwa tare da warware matsalolinsu yadda ya kamata. Game da wannan, Hong Lei ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen kara fahimtar juna, yin shawarwari, hadin gwiwa, warware matsaloli da kuma inganta dangantaka dake tsakaninsu yadda ya kamata. (Zainab)