A daidai lokacin, jimillar kudin cinikayyar bangarorin biyu,wato tsakanin kasashen Sin da Amurka za su zarce dalar Amurka biliyan 1000.
Yanzu, kasar Sin na kyautata hanyar da take bi wajen raya tattalin arziki, daga hanyar kara fitar da kayayyaki zuwa kara yawan bukatun sayayya a gida, kuma a maimakon ta kara saka jari, ta mai da hankali game da fannin kirkire-kirkire. Idan kasar Sin ta cimma burinta cikin shekaru 10 masu zuwa, tabbas za ta zama kasuwar duniya, ba kamar matakin gaba na masana'antun duniya da take kai yanzu ba.
Rahoton ya yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2022, kasar Sin za ta cike gurbin kasashen Canada da Mexico, kuma za ta zama kasar da ta shigar da kayayyaki mafi yawa daga kasar Amurka. Haka kuma, yawan kudaden kayayyakin da Sin ta fitar ga kasar Amurka, zai kai dalar Amurka biliyan 805.(Bako)