Bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi mai zurfi game da kafa dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka ta sabon nau'i da batutuwa masu daukar hankalin jama'a, da hana yaduwar makamai daga dukkan fannoni, kuma sun amince da yin shawarwari da hadin gwiwa bisa inuwar girmama juna da samun moriyar juna, da kafa amincewar juna bisa manyan tsare-tsare da karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, don dukufa ka'in da na'in wajen tabbatar da zaman lafiya da karko a duk duniya da shiyya-shiyya.(Bako)