Geng Yansheng ya nuna cewa, kasar Sin na nacewa kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da bin manufar tsaron kasa bisa ka'idar kare kanta. Kasar Sin ta zuba kudi kan aikin tsaron kasa ne domin kiyaye ikon mulkin kasa, tsaron kasa da cikakkun yankunan kasa, wanda shi ne halataccen ikonta a matsayinta na kasa. Don haka Amurka ba ta da ikon yi wa kasar Sin tsegumi ta fuskar aikin tsaron kasa da raya sojojin kasarta yadda ya kamata.
Har wa yau mista Geng ya ce, kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasa, batu ne da ya shafi babbar moriyar ko wace kasa. Sojojin kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasa. Rahoton Amurka ya mayar da baki fari, tare da dauke hankalin kasa da kasa, lamarin da ya nuna cewa, Amurka ba ta sauke nauyi yadda ya kamata ba.
Haka zalika, mista Geng ya jaddada cewa, a shekarun baya, an cimma babban tudun dafawa a jere wajen kyautata dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, an kuma shiga sabon hali na raya dangantakarsu cikin ruwan sanyi. Amma da gangan Amurka ta yi shaci-fadi kan barazanar da wai babban yankin kasar Sin ke kawo wa yankin Taiwan, ta haddasa tunzuri a tsakanin gabobin 2, a kokarin neman hujjar sayar wa Taiwan makamai, lamarin da kasar Sin ba ta yarda da shi ba ko kadan.
Sa'an nan kuma, kakakin ya ce, yanzu haka shugabannin kasashen 2 sun cimma muhimmin ra'ayi daya dangane da kokarin kafa hulda ta sabon salo a tsakanin manyan kasashe, amma gabatar da irin wannan rahoto da Amurka ta yi ya lahanta amincewa da juna a tsakaninsu. Kamata ya yi Amurka ta nuna sahihanci da kuma daukar hakikanin matakai wajen raya huldar da ke tsakanin sojojin kasashen 2 yadda ya kamata.(Tasallah)