Hua Chunying ta bayyana hakan ne sakamakon wani labari cewa, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta gabatar da wani rahoto game da aikin soja da tsaro na kasar Sin na shekarar 2013 a kwanakin baya. Kana Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan bin hanyar zaman lafiya don samun bunkasuwa, da manufofin tabbatar da tsaron kasa, a kasancewarta wata kasa mai karfi wajen kiyaye zaman lafiya a nahiyar Asiya da yankin tekun Pasific, har ma a duniya baki daya. Ban da wannan kuma, kamata ya yi kasar Sin ta gudanar da ayyukan tabbatar da tsaron kasa bisa halin da ake ciki a kasar, ta haka ne za ta iya tabbatar da 'yancin kai, ikon mallaka da kuma cikakkun yankunan kasar. (Zainab)