in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka za su gana da juna a wajen hutawa na Annenberg dake Amurka
2013-05-29 20:50:04 cri
A ranar Laraba 29 ga wata, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin, Zheng Zeguang ya bayyana cewa, an zabi wajen hutawa na Annenberg dake jihar California ta Amurka, a matsayin wurin da shugabannin Sin da Amurka za su gana da juna, abin da ya yi nuni da cewa, dangantaka tsakanin kasashen biyu na da muhimmanci na musamman.

Game da ziyarar shugaban Sin Xi Jinping a kasashe uku dake nahiyar Latin Amurka, da ganawarsa da shugaban Amurka, Mr. Zheng ya yi bayanin cewa, bayan yin shawarwari tsakaninsu, Sin da Amurka suna ganin cewa, wannan shiri ya dace sosai.

Don haka bangarorin biyu suna fatan shugabanninsu za su gana da juna tun da wuri, a kokarin yin musayar ra'ayi da shiri kan bunkasuwar dangantaka tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China