An kaddamar da shawarwari na taro na 12 na kwamitin zartaswa na shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai SCO a ranar 7 ga wata a nan birnin Beijing, kuma a matsayin shugaban karba-karba na kungiyar, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya jagoranci taron, kuma ya yi jawabi, inda ya nuna alkiblar raya kungiyar SCO daga fannoni 4.
Mr. Hu ya ce, taron koli na Beijing na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ya kasance taron koli na farko cikin shekaru goma-goma a karo na 2 bayan da aka kafa kungiyar, kuma a gun taron, za a kara tsara shirin raya kungiyar, kuma an yi imani cewa, a karkashin kokari na kasashen da abin ya shafa, za a cimma nasara a gun taron, kuma za a kara kuzari wajen raya kungiyar.
A cikin jawabinsa, Mr. Hu ya nuna alkibla wajen raya kungiyar SCO, wato a raya kasashen kungiyar don su zama wurare masu jituwa, da ba da tabbaci wajen shimfida zaman lafiya a yankin, da kokarin raya tattalin arziki na yankin, da kafa wani dandali mai amfani wajen yin mu'amala tsakanin kasashen kungiyar da kara karbuwansa a duniya.
Bugu da kari, Mr. Hu ya ce, game da harkokin gida na kasashen kungiyar SCO, dole ne jama'ar kasashensu su mallaki kansu, kuma ba'a yarda da sauran kasashen waje su yi shisshigi game da harkokin gida na kasashensu ba, kuma ana goyon baya ga kokarin da ake yi wajen kiyaye cin gashin kai da cikakken yanki da zaman lafiya da karko a yankin.(Bako)