An kaddamar da dandalin tattauna kan masana'antu da ciniki na kungiyar tattaunawar hadin kai ta birnin Shanghai SCO bisa jigon "zurfafa hadin kai a wannan shiyya, sabon hanyar ci gaba" a safiyar ran 6 ga wata a nan birnin Beijing. Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Qishan ya halarci bikin bude taro, inda ya nuna cewa, bisa burin tinkarar kalubaloli daban-daban, Sin na fatan mambobin kasashen SCO su tabbatar da tsare-tsaren hada kai ta fuskar cinikayya tsakaninsu da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki a wannan shiyya.
Wang Qishan ya nuna cewa, yanzu, mambobin kasashe suna tinkarar matsalar hada-hadar kudi yadda ya kamata tare da farfado da tattalin arzikin cikin sauri, wannan ya bada zarafi mai kyau wajen yin hadin kai a wannan shiyya.(Amina)