in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta) An gudanar da taron koli na kungiyar SCO a birnin Astana
2011-06-15 20:54:55 cri

A ran 15 ga wata a Astana, babban birnin kasar Kazakhstan, an gudanar da taron koli karo na 11 na kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai (SCO), inda shugaban kasar Sin Hu Jintao, da shugabannin kasashen Kazakhstan, Rasha, Kyrgyzstan, Tajikistan da Uzbekistan suka halarci taron.

Bana shekara ce ta cika shekaru 10 da kafa kungiyar SCO. A gun taron koli a wannan karo, shugabannin kasa da kasa za su yi nazarin fasahohin da kungiyar ta samu a shekaru 10 da suka gabata, kana za su tsara jadawalin aikin kungiyar na shekaru 10 masu zuwa.

A gun taron, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi jawabi, tare da bada shawarwari 4 game da shirin raya kungiyar na shekaru 10 masu zuwa, da suka hada da ci gaba da sada zumunci a tsakanin kasa da kasa don kafa wani yanki mai jituwa, da kara karfin tinkarar barazana don tabbatar da zaman lafiya a yankin, da sa kaimi ga raya tattalin arzikin yankin ya zamo na bai daya a kokarin samun ci gaba tare, kana da kara yin hadin gwiwa a fannin al'adu da kiyaye dangantakar abokantaka a tsakanin jama'ar yankin har abada.

Ban da wannan kuma, Hu Jintao ya yaba da nasarorin da kungiyar SCO ta samu a shekaru 10 da suka gabata.

Haka kuma, a gun taron, an daddale sanarwar Astana, inda mambobin kungiyar suka cimma daidaito game da yin hadin gwiwa tsakaninsu ta fuskokin tsaro da raya tattalin arziki da sauransu.

Haka kuma, a cikin sanarwar, an bayyana cewa, babban burin da ke akwai ga kungiyar shi ne inganta zaman rayuwa da kawo alheri ga jama'arta, haka kuma an nuna cewa, wannan kungiya za ta inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobinta wajen al'adu, kiyaye muhalli, kimiyya da fasaha, da motsa jiki, da ci gaba da yin hadin gwiwa tsakaninsu wajen magance kalubalen da bala'I daga indallahi kan kawo.

Ban da wannan kuma, a cikin sanarwar da mambobin kungiyar SCO suka bayar, an jaddada cewa, dole ne a samo hanyar dakatar da rikicin da ake yi a kasar Libya, kuma kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su dauki matakai bisa kuduri mai lamba 1970 da na 1973 da kwamitin sulhu na M.D.D ya zartas da su.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China