in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai kungiya ce dake tafiya da zamani, in ji shugaban kasar Sin
2012-06-06 15:36:41 cri
Kafin bude taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai(SCO), kwanan baya yayin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ke hira da 'yan jaridar kasashen wannan kungiya, ya ce, nasarorin da kungiyar ta cimma sun shaida cewa, kungiyar tana samar da tabbaci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, haka kuma tana sa kuzari ga bunkasuwar kasashen shiyyar, wadda dalilin haka ta kasance kungiyar shiyya shiyya dake tafiya tare da zamani.

Mr.Hu Jintao ya ce, nan da shekaru 10 masu zuwa, za mu ci gaba da dora muhimmanci a kan hadin gwiwa ta fannin tsaro, tare da inganta mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobin kungiyar, a kokarin samar da yanayi mai kyau a kasashen shiyyar, ta yadda kungiyar za ta kasance wani tsarin da zai iya tabbatar da tsaron mambobinta da inganta hadin gwiwa da kuma karfafa dankon zumunci a tsakaninsu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China