Za a shafe kwanaki biyu ana gudanar da taron. Da farko, shugabannin kasashe membobin kungiyar SCO guda 6 wato Sin, Rasha, Kazakhstan, Kyrgyz, Tajikistan da kuma Uzbekistan sun yi shawarwari na sa'a daya a ranar 6 ga wannan wata da yamma. Kafin shawarwarin, shugabannin kasashen 6 sun dauki hoto tare. Bayan da aka kammala shawarwarin, shugaban kasar Sin Hu Jintao zai shirya wata liyafa don maraba da zuwan shugabannin kasashen da suka halarci taron kolin kungiyar na Beijing.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a bayar da wata sanarwa game da yadda za a shimfida zaman lafiya da samun wadata tare a gun taron koli na Beijing, da tabbatar da wani buri na inganta yankin kasashe membobin kungiyar SCO zuwa wani yanki mai jituwa, da kuma cimma ra'ayi daya a tsakanin kasashe membobin kungiyar kan manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna.(Zainab)