Imanaliev ya fadi haka ne, yayin da ya halarci bikin baje-kolin kayayyakin Asiya da Turai a karo na farko da taron tattaunawar hadin gwiwar raya tattalin arziki na kasashen Asiya da Turai da kasar Sin ta shirya.
Haka kuma Imanaliev ya bayyana cewa, jihar Xinjiang na yin mu'amalar tattalin arziki da cinikayya da mambobin kasashen kungiyar SCO cikin aminci, kuma ana yin hadin gwiwa da mu'amalar tattalin arziki tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin tsakiyar Asiya ta hanyar Xinjiang, kuma taron baje-koli da aka shirya a wannan karo a Xinjiang zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin mambobin kasashen kungiyar SCO.(Bako)