Kasancewarsa wani muhimmin bangare na taron baje koli tsakanin kasar Sin da kasashen Asiya da Turai, taron kasuwanci na kungiyar SCO ya zama wani muhimmin dandali wajen yin mu'amala da tattauna hadin gwiwa a tsakanin kasashen mambobin kungiyar SCO.
Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Li Jinzao ya halarci bikin bude taron tare da yin jawabi, inda ya bayyana cewa, bayan da aka kafa kungiyar SCO yau kusan shekaru 11 ke nan, kungiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta hakikanin hadin gwiwa a wannan yanki. A shekarar 2011, yawan cinikin da ke tsakanin kasar Sin da sauran kasashen mambobin kungiyar SCO ya zarce dalar Amurka biliyan 100, abin da ya karu da kashi 35 cikin 100. haka kuma hadin gwiwar tattalin arziki na shiyya-shiyya ya shafi fannonin muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a na zamani da raya birane da tattalin arziki da zamantakewar al'umma, a sa'i daya kuma, an gaggauta raya hadin gwiwa a fannonin sufurin kayayyaki da raya kimiyya da fasaha, ta yadda za a kara azama ga raya tattalin arziki na shiyya-shiyya.
Haka kuma, Li Jinzao ya ce, kasar Sin tana fatan yin kokari da bangarorin da abin ya shafa, don sa himma wajen kirkiro wani sabon salo na yin hadin gwiwa tsakaninsu, da karfafa hadin gwiwa da kasashe mambobin kungiyar SCO, don kara ba da gudummawa wajen kawo dauwamammen zaman lafiya da samun bunkasuwa a wannan yanki.(Bako)