in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya bayar da shawarar dora muhimancin hadewar tsarin kayayyakin more rayuwar shiyyar waje guda
2012-12-05 20:08:45 cri
Firaministan kasar Sin Wen Jiabao, ya ba da shawara a ranar Laraba cewa, kamata ya yi kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) ta yi kokarin bayar da muhimmanci wajen hada tsarin kayayyakin more rayuwar shiyyar karkashin laima guda.

Wen ya fada a yayin da ya ke jawabi a taron firaministocin kungiyar karo na 11 cewa, kamata ya yi a yi la'akari da shirin tare da tsara shi ta hanyar kimiya, yin amfani da manufofin da masana'antu ke aike da su, sannan kasuwanni su tafiyar da shi don tabbatar da ingancin tsarin.

Ya ce kasar Sin a shirye take ta bunkasa hadin gwiwa da kasashe mambobin kungiyar a kokarin da take na cika alkawarin da ta dauka a watan Yuni na samar da rancen dala biliyan 10 ga sauran mambobin kungiyar.

Bugu da kari Mr. Wen ya yi magana kan kafa cibiyar da za ta samar da yanayin da ya dace tsakanin Sin da kungiyar ta SCO domin karfafa tsarin kiyaye yanayin da ake ciki.

Don haka ya yi kira ga mabobin kungiyar ta SCO, dasu hada karfi da karfe domin yaki da matsalolin ke hana ruwa gudu, kamar fataucin kwayoyi, ayyukan ta'addanci da ake aikatawa a kan iyakokin kasashen kungiyar, tare da kafa wata cibiyar yin gargadin abkuwar bala'u da samar da ceto, kana a aiwatar da shirin hadin gwiwa na samar da abinci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China