Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa birnin Saint Petersburg na kasar Rasha a ran 6 ga wata da yamma, domin halartar taron firaministoci na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a karo na 10.
A gun taron, firaministan Sin Wen Jiabao zai takaita halin da ake ciki na ci gaban yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen kungiyar a cikin shekarar da ta wuce tare da sauran firaministoci, kana za su tattauna kan yanayin kasa da kasa da na shiyya-shiyya da tsara fasalin hadin gwiwarsu na nan gaba a fannonin tsaro da tattalin arziki da al'ada da sauransu bisa matsayin da aka cimma a gun taron koli na Astana da aka yi a watan Yuni na wannan shekara.
An kafa kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a shekarar 2001, wadda ta hada da kasashe 6 wato kasashen Kazakhstan da Sin da Kirghizstan da Rasha da Tadzhikistan da kuma Uzbekistan. Kana kasashen Mongolia da Pakistan da Iran da India su 'yan kallo ne na kungiyar.(Lami)