Kotun shigar da kara ta Alkahira ta yanke hukunci a ran 21 ga wata bisa agogon wuri, inda ta yarda da ba da belin tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak.
Kotun ta yankewa Mubarak hukunci ne bisa zargin da aka yi masa na karbar kyautar kudin da ya kai miliyoyin kudin Masar daga kafar watsa labarai ta kasar.
Sakin shi da kotu ta yi ba ta bayyana cewa Mubarak ba shi da laifi ba , to amma bisa dokokin wuri, ba za a iya tsare da mutum sama da shekaru biyu ba, don haka, za a ba da belin shi. Kafar yada labaru ta kasar ta ba da labari cewa, ba za a yarda da Mubarak ya bar kasar Masar ko maido da dukkiyarsa ba, duk da cewar an sake shi.
An ce, an saki Hosni Mubarak makonni 7 bayan da sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi, abin da zai iya fusata jama'a daga wasu sassa, kana zai kawo cikas ga samun sulhu tsakanin al'umma. (Amina)