Bisa labarin da gidan talebiji na kasar Masar ya bayar, an ce, an tsare Hosni Mubarak, yaransa, tsohon ministan kula da harkokin gida na kasar Habib Adli da 'yan sanda 6 tare. Kafin Hosni Mubarak ya isa birnin Alkahira, magoya bayansa da 'yan adawa sun yi arangama a kofar kotun, 'yan sanda fiye da dubu ne ke tsaron kofar kotun.
An soma tuhumar Hosni Mubarak kan laifuffukan da ya aikata ne a Alkahira a wannan rana da karfe 10 na safe bisa agogon birnin Alkahira. Kuma an yi zargin cewa Hosni Mubarak ya yi amfani da mulkinsa wajen aikata almundahana, da ba da umurnin kashe masu zanga-zanga yayin da jama'ar kasar suka yi zanga-zanga.
A ran 25 ga watan Janairu, an yi zanga-zanga a kasar Masar don nuna adawa da gwamnatin Mubarak. Kuma a ran 11 ga watan Faburairu, Hosni Mubarak ya sauka daga mukaminsa, kana aka tsare shi a Sharm El-Sheikh.(Mubarak)