in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon shugaban kasar Masar, Mubarak ya sake zuwa kotu dongane da sake shari'a kansa
2013-04-13 16:22:29 cri
Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya isa makarantar 'yan sanda dake wajen birnin Alkahira ranar Asabar da safe, dangane da sake sharia'a da za'a yi masa, in ji gidan talbijin din kasar.

'Ya'yansa guda biyu, Alaa da Gamal da kuma tsohon ministan harkokin cikin gida na kasar Habib Al-Adly su ma duka sun bayyana a kotun suna jiran a sake shari'ar.

A halin yanzu dai Mubarak na cikin daurin rai da rai da aka yi masa saboda hukuncin da aka yanke masa cewa, yana da hannu a kisan masu zanga zanga da aka yi cikin watan Janairun 2011 da ma sauran tuhuma na cin rashawa da wawurar kudade. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China