in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohuwar shugabar kasar Afrika ta Kudu ta zama direktar hukuma mai kula da harkokin mata ta MDD
2013-08-20 14:11:58 cri

Tsohuwar shugabar kasar Afrika ta Kudu Madam Phumzile Mlambo-Ngcuka ta yi rantsuwar kama aiki a matsayin direktar gudanarwa ta hukuma mai kula da harkokin mata ta MDD a ran 19 ga wata a birnin New York inda hedkwatar majalisar ke zama.

Babban sakataren MDD Mr. Ban Ki-Moon ya ba da jagoranci ga bikin rantsuwa a wannan rana. Phumzile Mlambo-Ngcuka ta aza hannunta na hagu a kan kundin tsarin mulkin MDD, kuma ta daga hannun dama dinta ta yi rantsuwar kama aiki a gaban Ban Ki-Moon. Bayan bikin, Ban Ki-Moon ya nuna kyakkyawar fata ga Phumzile Mlambo-Ngcuka, kuma ya ba ta hatimin MDD.

An ba da labari cewa, an kafa hukuma mai kula da harkokin mata ta MDD ne a watan Yuli na shekarar 2010, tare da aniyar kara azama ga aikin samun daidaito a tsakanin maza da mata, da kuma ba da kariya ga hakkin mata, ta yadda za a iya kiyaye muradunsu yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China