Wata sanarwa da mai Magana da yawun magatakardan na MDD ya bayar na mai bayyana cewa Magatakardan ya damu matuka dangane da abubuwa dake aukuwa a kasar Masar da kuma bazuwar barkewar rikici kana da amfani da karfin tuwo wajen shawo kansu.
Cikin sanarwar Mr Ban yayi suka da kakkausar murya kan harin da aka kai a majami'u, asibitoti da sauran wuraren jama'a inda yace ko kadan hakan bai dace ba. (Lami Ali Mohammed)