in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta yi hadin gwiwa da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya a fuskar kiyaye zaman lafiya
2013-08-07 10:36:42 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya ba da sanarwar shugaba a ran 6 ga wata cewa, MDD za ta kara hadin kai da wasu kungiyoyin shiyya-shiyya da ma sauran kungiyoyi, a fuskar yin rigakafin barkewar rikici, kiyaye zaman lafiya, hana yaduwar makaman kare dangi, shari'a da doka da dai sauransu.

A wannan rana kuma, kwamitin ya yi babbar muhawara tare da ba da shawarar shugaba, kan hadin gwiwa tsakanin MDD da wasu kungiyoyin shiyya-shiyya, inda aka nuna cewa, kwamitin na maraba da matakan da ake dauka wajen yin hadin gwiwa.

A gun taron, babban sakataren MDD Mr Ban Ki-Moon ya yi kira da a kara hadin gwiwa da yin mu'ammala tsakanin kungiyoyin shiyya-shiyya da sauran kungiyoyi.

Ban da haka, a wannan rana kuma, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya ba da jawabi cewa, ya kamata, kwamitin ya sa kaimi ga mu'ammala, da sulhu tsakanin wadannan kungiyoyi ta yadda za su warware wasu rikice-rikice ta hanyar lumana, da kuma ba da gudunmawa wajen shimfida zaman lafiya a yankin.

A sa'i daya kuma, ya kamata, wadannan kungiyoyi su gudanar da aikinsu bisa tsarin ka'idar MDD, da kuma daukar wasu matakan na dole bisa ka'idar kwamitin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China