Mista Wanda-Kasibwe, dake mashawarcin musammun na shugaban kasar Uganda kan harkokin al'umma da kiwon lafiya, kuma shugaban kwamatin zartarwa na asusun kamfanin Center Ltd, zai maye gurbin 'yar kasar Tanzania madam Asha-Rose Migiro, a cewar wata sanarwa ta kakakin Ban Ki-moon.
A tsawon shekarun baya bayan nan, nahiyar Afrika ta samu babban cigaba a cikin yakinta da wannan bala'in ciwo.
A cewar wasu alkaluman MDD na shekarar 2011, a kalla an samu raguwar kashi 32 cikin 100 na yawan mutuwar mutane dake da nasaba ciwon Sida a Afrika idan aka kwatanta dana shekarar 2005 haka, sannan kuma yawan mutanen da suka fara kamuwa da cutar na ragu da kashi 33 cikin 100 a shekarar 2011 idan aka kwatanta da na shekarar 2001.
Sai dai duk da haka, Afrika ta kasance nahiyar data fi fama da cutar kanjamau. Bisa yawan mutane miliyan 34 dake dauke da kwayoyin wannan cuta a duniya, miliyan 23.5 suke rayuwa a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, wato kimanin kashi 69 cikin 100 na wadannan mutane. (Maman Ada)