in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya nada sabon mataimakin shugaban shirin muhalli na MDD
2013-08-03 16:30:15 cri
A ranar Jumma'a magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya nada Ibrahim Thiaw na kasar Mauritaniya a matsayin mataimakin babban sakatare kuma mataimakin babban darekta na shirin kula da muhalli na MDD (UNEP).

Thiawa wanda a yanzu haka shi ne darekta a sashen aiwatar da manufofi na shirin kula da muhalli na MDD, UNEP zai maye gurbin Amina Mohammed 'yar kasar Kenya, bisa sanarwar da ta fito daga hannun mai magana da yawun Mr. Ban.

Sanarwar ta ci gaba da baiyana cewa Thiaw ya shafe shekaru sama da talatin yana aiki a fannin kula da muhalli da dorewar bunkasa ga kuma sani da yake da shi na harkokin shirin na UNEP da dai sauran fannoni.

Thiaw ya fara aiki a wannan fuska ne a kasarsa ta Mauritaniya inda ya shafe shekaru 10 a ma'aikatar bunkasa karkara, a fadin sanarwar. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China