Kungiyar 'yan adawa ta kasar Sham da masu goyon bayanta sun bayyana cewa, tilas ne shugaba Assad ya sauka daga mukaminsa, kana bai kamata a baiwa masu goyon bayansa mukami a hukumomin gudanarwa na wucin gadi na kasar ba. Har ila yau Jarba ya yi kira ga kasashen duniya da su kara matsin lamba ga shugaba Assad don tursasa shi amincewa da shirin warware rikicin kasar ta hanyar siyasa. Amma zaunannen wakilin kasar Rasha dake MDD Vitaly Churkin ya bayyana cewa, sanya wannan bukatu cikin sharadin gudanar taron na Geneva, zai kara shigar da shirin cikin mawuyacin hali. (Zainab)