Kudurin ya ce, kwamitin sulhu na MDD ya bukaci bangarori daban daban na Darfur, musamman ma duk wadanda ba su sa hannu kan yarjejeniyar Doha ba, da su yi alkawarin cimma matsaya guda na dakatar da bude wuta har abada bisa iyakacin kokarinsu ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Ban da haka, kudurin ya bukaci bangarorin daban daban masu ruwa da tsaki a rikicin Darfur da su daina nuna karfin tuwo ga fararen hula da ma'aikata masu kiyaye zaman lafiya da masu jin kai, kuma ya bukaci gwamnatin Sudan da sojoji da dakaru masu dauke da makamai da sauransu da su tabbatar da shige da ficen kungiyoyin ba da taimakon jin kai da masu ceto a yankunan da ake samun abkuwar rikici yadda ya kamata.(Fatima)