in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi maraba da soke takunkumi kan kasar Iraki
2013-07-02 16:35:19 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lambar 2107 dake soke takunkumin da aka kakabawa kasar Iraki tun lokacin mulkin shugaba Sadam Hussein bisa babin bakwai na ka'idojin MDD, game da wannan mataki, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a ranar 2 ga watan Yuli a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin tana farin ciki sosai da labarin zartas da wannan kuduri, kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga MDD wajen warware matsalolin da abin ya shafa. Kasar Sin na mai da hankali sosai kan gina dangantakar abokantaka tare da kasar Iraki, tare da fatan ci gaba da bunkasa dangantakar sada zumunci tsakanin kasashen biyu bisa tushen nuna adalci da cimma moriyar juna. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China