A wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin Shen Danyang ta taya wa Li Yong murnar lashe wannan zabe. Kana ta nuna cewa, kasar Sin ta gabatar da dan takarar da ya shiga zaben babban direktan hukumar UNIDO a wannan karo, abin da ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya ga inganta sha'anin bunkasa kasa da kasa, musamman sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa.
Ban da wannan kuma, Shen Danyang ta jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa a tsakaninta da hukumar UNIDO, a kokarin sa kaimi ga hukumar da ta kara ba da gudummawa wajen samun bunkasuwa mai dorewa a fadin duniya.
An kafa hukumar UNIDO ne a shekarar 1966, wadda ta kasance wata hukumar musamman ta MDD a shekarar 1985. A halin yanzu, akwai membobi 172 a hukumar, cibiyarta tana birnin Vienna, inda babban direkta ke shugabantar babban hukumar. Makasudin hukumar shi ne taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun dauwamammiyar bunkasuwa kan masana'antu da kuma sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. (Zainab)