in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya da kuma shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD
2013-06-27 11:05:24 cri
A ran 26 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya da shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, da kara ba da babban taimako domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wani taro a bainar jama'a kan batun ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a wannan rana, inda Wang Min ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana samun sauye-sauye a duniya, kuma ana fuskantar barazana da kalubale a fannin zaman lafiya da tsaro a duniya ta hanyoyi daban daban. Don dacewa da sauyin yanayin da ake fuskanta a duniya, ana kara kyautata da yin kwaskwarima kan ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. Hakazalika kuma, ana samun matsaloli kamar yadda za a bada izni ga ayyukan kiyaye zaman lafiya, sarrafa ayyukan da kuma tabbatar ganin an samu sakamakon ayyukan da dai sauransu.

Wang Min ya kara da cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya ga kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin cibiyar MDD da tawagogin musamman na MDD, da kuma tsakanin hukumomin tawagogin, da tabbatar da aiwatar da tsarin bada umurni yadda ya kamata. Game da batun harin da aka kaiwa masu aikin kiyaye zaman lafiya, wanda ya kawo hasara ga kasar da ta tura sojojinta da kuma kawo illa ga ayyukan tawagogin musamman, kamata ya yi MDD ta kara sa lura kan batun, da kuma kara daukar matakan tabbatar da tsaron ma'aikatan kiyaye zaman lafiya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China