Dramane Dembélé ya bayyana hakan ne yayin wani taron 'yan jaridu da aka yi ranar Asabar 3 ga wata, a birnin Bamako, hedkwatar kasar ta Mali. Dembélé ya ce, tuni ya riga ya kammala shawarwari da Kéita a ran 2 ga wata, inda kuma suka cimma matsaya guda. Bisa kuma hakan ne shi da jam'iyyarsa da take a matsayi na uku a sakamakon zaben za su goyi bayan PRM a zagayen zaben na gaba.
An dai gudanar da babban zaben shugaban kasar Mali a zagaye na farko ne a ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata, inda masu kada kuri'a miliyan 6.88 sun jefa kuri'a ga 'yan takara 27. An kuma kammala wannan zagaye na farko lami lafiya. (Fatima)