Bisa dokokin zaben kasar Mali, an ce, ya kamata gwamnatin kasar ta sanar da sakamakon farkon zabe cikin kwanaki 5 bayan jefa kuri'u, kuma, ranar 2 ga wata, ya zama ranar karshe da ya kamata a sanar da sakamakon. sannan a gabatar da sakamakon ga koton tsarin mulkin kasar don ya tabbatar da sakamakon.
A baya dai, an sanar da sakamakon farkon babban zaben shugaban kasa na zagayen farko ran 30 ga watan Yuli, inda ya nuna cewa, dan takarar zaben da ya fito daga jam'iyyar kawancen kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ke kan gaba da ya samu kuri'u sama da kashi 50 bisa dari, idan aka tabbatar da sakamakon mista Keita zai kasance ke nan shi ya lashe zaben. Amma abokin hamayyarsa mista Soumaila Cisse, tsohon ministan harkokon kudin kasar ya bayyana cewa, an aikata magudi lokacin babban zaben, shi ya sa ya kamata a gudanar da zaben zagaye na biyu.
Shugaban wucin gadi na kasar Mali Dioncounda Traore da kuma babban sakataren MDD Ban Ki-moon sun yi kira ga jama'ar kasar Mali da su girmama sakamakon zabe na karshe. (Maryam)