Wannan shiri mai taken "kyautata matsayin mata bisa takardun sunayen 'yan takara domin zabukan shekarar 2013 zuwa shekarar 2014" da kuma "kasidar rigakafi ta mata domin ganin an gudanar da zabuka cikin zaman lafiya da adalci a kasar Mali", sun samu tallafin kudi daga MDD da kungiyoyin ba da tallafi.
Wadannan ayyuka biyu na gudana a karkashin jagorancin kungiyar sasanta 'yan kasa da tabbatar da demokaradiya ta kasar Mali (CMDID) da kuma gungun Pivot na yanci da kishin kasa na Matan kasar Mali.
Haka kuma baya ga manyan jami'an wadannan shirin, bikin kaddamarwar ya samu halartar wakiliyar ofishin ministan iyali da wakilin ma'aikatar hukumomin kasa, shugaban kwamitin sasanta 'yan kasa, Mohamed Salia Sokona da kuma wakiliyar tawagar MINUSMA dake kasar Mali. (Maman Ada)