in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata mace za ta shiga takarar shugaban kasar Mali
2013-06-17 16:55:37 cri

A kwanan baya, membar majalisar dokokin kasar Mali, Aissata Cisse Haidara ta sanar da cewa, za ta shiga takarar zaben shugaban kasar a ranar 28 ga watan Yuli. Wannan ne karo na farko da wata mace ta shiga takarar shugaban kasar Mali a tarihi.

A kwanakin baya Madam Aissata Cisse Haidara ta kira wani taron magoya bayanta, inda ta bayyana cewa, yanzu abin dake gaban kome shi ne farfado da kasar Mali, musamman ma yankin arewa. Amma a sa'i daya, dole ne a kula da jam'iyyu daban daban dake kudancin kasar, a kokarin tabbatar da hadin kan kasar baki daya. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China