Dan takarar Jam'iyyar RPM a kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita da aka fi sani da IBK ya shiga gaban abokan takararsa da fiye da hamsin cikin dari na kuri'un da aka jefa a zaben shugaban kasar Mali na ranar 28 ga watan Yuli, sakamakon da aka ba da kidayar kashi daya cikin kashi uku na kuri'u na wannan zaben shugaban kasa, in ji ministan hukumomin kasar Mali, kanal Moussa Sinko Coulbaly a yayin wani bikin bada sakamakon zabe na wucin gadi.
« Muna bisa kashi daya cikin kashi uku na kidayar kuri'un da aka jefa. Sakamako na zuwa sannu a hankali daga yankunan kasar da kuma ketare. Bisa alkaluman da aka samu na yanzu, Ibrahim Boubacar Keita da aka fi sani da IBK ke kan gaba tare da fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka jefa, sannan mai bi masa Soumaila Cisse na jam'iyyar URD, a gaban dan takarar jam'iyyar ADEMA, mista Dramane Dembele », in ji minista Coulbaly tare da bayyana cewa, aikin kidayar zai kare ranar yau Laraba. Haka zalika ministan hukumomin kasar Mali ya nuna cewa, idan har tazara sosai tsakanin wadannan 'yan takara ta tabbata to ba za'a je ga zagaye na biyu ba. (Maman Ada)