Yayin taron manema labarai da aka yi a wannan rana da yamma, babban birnin kasar Mali, Mr. Kufour ya nuna cewa, an gudanar da zagayen farko na jefa kuri'u cikin yanayin zaman lafiya, kuma jama'ar kasa sun hallara don jefa kuri'u cikin himma da kwazo.
Ya kara da cewa, ko da yake an nuna damuwa sosai dangane da matsalar katin masu zabe, duk da hakan ba a aikata magudi ba yayin jefa kuri'un. Ya kuma yi kira ga jama'ar kasar Mali da su nuna hakuri wajen jiran sakamakon zaben wanda gwamnatin kasar za ta sanar a hukunce.
An fara jefa kuri'u na zagayen farko na babban zaben shugaban kasar Mali ran 28 ga wata da safe, kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta tura masu sa ido kan babban zaben guda 250 zuwa manyan yankuna guda 8 na kasar.
Tuni dai aka fara kidaya bayan da aka kammala jefa kuri'a, kuma za a sanar da sakamako a ranar 2 ga watan Agusta a hukunce.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ba da sanarwa inda ya taya kasar Mali murnar gudanar da babban zaben cikin yanayin zaman lafiya, inda ya kara da cewa, babban zaben zai ba da taimako wajen farfado da tsarin mulkin kasa, bayan nasara da kasar ta cimma na yaki da 'yan ta'adda da kuma samun 'yancin kai a duk fadin kasar. (Maryam)