Nesirky ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai, inda ya ce, ofishin babbar kwamishinar kula da 'yan gudun hijira ta MDD(UNHCR) ya bayyana cewa, yana ci gaba da shiryawa tare da hukumomin kasar Mali da sauran kasashe makwabtaka, ta yadda wadanda ke gudun hijira za su kada kuri'unsu.
Kakakin na MDD ya ruwaito UNHCR din na cewa, yana da muhimmanci mahukuntan kasar ta Mali su hanzarta baje kolin rijistar masu zabe da raba katunan zabe a Burkina-Faso, Niger da Mauritania.
A cewar UNHCR, an yi kiyasin cewa, yawan 'yan gudun hijirar Mali da ke kasashen Burkina-Faso, Niger da kuma Mauritania sakamakon fadan Mali na baya-bayan nan ya kai 175,000.
Nesirky ya ce, rawar da hukumar za ta taka yayin zaben, ita ce taimakawa 'yan gudun hijira su yi zabe cikin yanayin tsaro. (Ibrahim)