Hukumomin rundunar sojojin tarayyar Najeriya sun bada sanarwa a ranar Talata 30 ga wata cewa, sun fara janye sojojin kasar dake cikin wasu ayyukan tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali. Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya, Chris Olukolade ya bayyana na cikin wata sanarwa cewa wannan shiri ya shafi musammun ma rukunonin sojojin da ba su cikin tawagogin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake kasar Mali na MINUSMA. Wadannan sojoji za su koma wajen ayyukan tsaron dake gudana a cikin kasar Najeriya, in ji jami'in tare da bayyana cewa wannan mataki an dauke shi ne bayan gyare gyaren da aka samu da karba nauyin aikin tawagar Afrika ta taimakon kasa da kasa a kasar Mali (AFISMA) da MDD ta yi. (Maman Ada)