A yayin jawabin da aka saba bayarwa ga 'yan jarida kowace rana, mai magana da yawun MDD Martin Nesirky ya baiyana cewa hukumar zabe ta kasar Mali ta sanar da sakamakon dake hannu, na zaben shugaban kasar da aka yi ranar 28 ga watan Yuli, to amma za'a baiyana cikakken sakamakon zaben ne bayan kotun dokokin kasar ta yi nazari.
Nesirky ya ci gaba da cewa an sanya ranar 11 ga watan Agustan da muke ciki a matsayin ranar da za'a yi zaben zagaye na biyu don fid da zakara tsakanin manyan 'yan takara guda biyu, kuma bisa tsarin ayyuka da aka damka mata, hukumar ta MDD a kasar Mali za ta ci gaba da samar da tsaro, da kuma tallafi, a wasu fuskoki kamar na kayan aiki da fasaha a yayin zaben.
Ya ci gaba da cewa hukumar a shirye take ta tallafawa mahukuntan kasar Mali kamar yadda za su bukaci hakan.
Kwamitin sulhu na MDD ne ya kafa hukumar hadin gwiwar tabbatar da daidaito a kasar Mali (MINUSMA) ranar 25 ga watan Aprilu shekarar da muke ciki.
Bisa muhimman kudurorin kwamitin sulhu, MINUSMA tana dauke da nauyin samar da tallafi ga shiron siyasa da kuma gudanar da wasu ayyukan tabbatar da dorewar tsaro a kasar ta Afirka. (Lami Ali)