Yana mai cewa, wannan tsari ya dace da garanbawul da Sin take yi a fannin tsarin sa ido da zartaswa, kuma hakan zai kawo amfani wajen samarwa kamfanoni wani yanayi mai adalci na yin takara tare, da kuma kara karfin kasuwanni ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.
Shen Danyang ya ce, yanzu akwai makoma mai kyau wajen raya dangantakar hadin gwiwa a fannin ciniki da tattalin arziki tsakannin kasashen Sin da Amurka, kuma yawan jarin da suke zubawa juna ya rika karuwa a fannoni daban-daban. Bangarorin biyu za su cimma moriyarsu yadda ya kamata muddin suka kai ga daddale wata yarjejeniyar kawo moriyar juna a fannin zuba jari. Sin na fatan hadin gwiwa da kasar Amurka don ciyar da shawarwarin gaba. (Amina)