A ranar 29 ga watan Afrilu, a gun taron manema labaru na ministocin tsaron kasashen Amurka da Japan cikin hadin gwiwa, Hagel ya bayyana cewa, Amurka na nuna adawa ga daukar matakin da za su lahanta hakkin mallakar tsibirin Diaoyu na Japan, kuma ya ce, yayin da babban hafsa-hafsoshi na Amurka Martin E. Dempsey, ke ziyara a birnin Beijing da ke kasar Sin, shi ma ya bayyana irin wannan ra'ayi. Game da wannan, a ranar 30 ga wata, Cui Tiankai ya mayar da martani, inda ya bayyana cewa, zancen da Hagel ya yi, don gane da ziyarar Dempsey da shawarwarin da ke tsakaninsa da kasar Sin bai dace da halin da ake ciki ba, a wancan lokaci, Sin ta bayyana matsayin da take kai game da batun tsibirin na Diaoyu, kuma Amurka ma, ta fahimci ra'ayin kasar Sin.(Bako)