Hillary ta bayyana cewa, daidaita dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka na da muhimmanci sosai, ko da yake akwai kalubale sosai, amma duk da haka, a cikin shekaru 4 da suka gabata, kyautata dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ya zama wani muhimmin aiki ga gwamnatin Obama, aikin da gwamnatin ta yi kokarin gudanarwa.
Haka kuma, ta bayyana cewa, Amurka na da imani cewa, kasashen Sin da Amurka za su kasance tare a yankin tekun Fasific, haka kuma yanzu Amurka na fatan ganin kasar Sin da ta dauki nauyin bisa kanta a cikin harkokin kungiyoyin duniya da na shiyya-shiyya, kuma tana fatan Sin za ta sauke nauyin da ke wuyanta wajen daidaita batun Asiya da tekun Fasific.
Hillary Clinton da ta jagoranci shawarwari bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Amurka cikin shekaru 4 da suka gabata, ta nuna cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su kiyaye ci gaba da aka samu, da ci gaba da yin musayar ra'ayi bisa sahihiyar zuciya.(Bako)