Bisa labarin da aka bayar a kan shafin internet na ma'aikatar tsaron kasar Sin, an ce, Qi Jianguo ya jaddada a gun shawarwarin cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan tabbatar da ikon mallakar kasar, cikakken yancin kasar da kuma moriyar kasar a kan teku.
Ban da wadannan kuma, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar sojojinsu, tsaron aikin soja a kan teku, zaman lafiyar kasashen duniya da yankuna da dai sauransu, musamman ma sun yi tattaunawa sosai kuma sun cimma matsaya daya a fannoni da dama kan yadda za a aiwatar da ayyuka da shugabannin kasashen biyu suka tsara, na inganta dangantakar sojojinsu da aikin sojansu a cikin yanayi da ake yanzu. (Zainab)