in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Japan ce ke daukar matakin da bai dace ba kan rikicin da ake game da tsibirin Diaoyu, a cewar manzon kasar Sin
2013-05-01 16:49:03 cri

Jakadan kasar Sin da ke Amurka Cui Tiankai ya fada a ranar Talata 30 ga watan jiya cewa, Japan ce ke daukar matakin da bai dace ba kan takaddamar da ke tsakanin Sin da Japan game da tsibirin nan na Diaoyu.

Mr. Cui ya yi wannan kalami ne, yayin da ya ke mayar da martani kan kalaman da sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ya yi game da takaddamar da ke tsakanin Japan da kasar Sin game da tsibirin Diaoyu.

Da yake jawabi ga taron manema labarai na hadin gwiwa a ranar Litinin tare da ministan tsaron Japan dake ziyara a Amurka Itsunori Onodera, Hagel ya ce Amurka ba ta goyon bayan duk wani matakin da bai dace ba wanda zai kaskantar da ikon Japan, sakon da shugaban hafsan hafsosin Amurka Janar Martin Dempsey ya gabatarwa Sin makon da ya gabata a Beijing.

A cikin wata hira da kafar watsa labaran Sin da ke Washington, Cui ya ce wasu daga cikin kalaman da Hagel ya yi game da ganawar da aka yi tsakanin Dempsey da bangaren Sin, ba su yi dai-dai da hujjojin da ya bayar ba.

Cui ya ce, bangaren Sin ya yi musayar ra'ayoyin sosai da Mr. Dempsey kan batutuwa dabam-dabam, kuma Sin ta bayyana matsayi da ra'ayinta karara. Kuma ya yi imanin cewa, tuni bangaren Amurka suna da masaniya game da ganawar, don haka kamata ya yi su fahimci gaskiyar lamarin yadda ya kamata.

Mr. Cui ya jaddada cewa, Japan ce ba Sin ba, ta haifar da yanayin zaman dar-dar da ake ciki, kuma take daukar matakin da bai dace ba game da batun tsibirin Diaoyu, wanda tarihi da shaidu suka nuna cewa wani bangare ne na Sin tun asali. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China