A cikin shawarwarin, kasashen biyu sun bayyana ci gaban da suka samu a wannan fanni, kuma sun yi musayar ra'ayi kan wasu manyan batutuwa ciki har da hada kai a fannin hakkin Bil Adama a duniya, tafiyar da harkokin mulki bisa doka, hakkin fadin albarkacin baki, nauyin da kafofin yada labaru suke da shi, batunbambancin launin fata da sauransu. Sin na fatan Amurka ta mutunta ikon mulkin kai, cikakken yankin kasar Sin da kuma mutunta tsarin siyasa, tsarin gudanar da shari'a da kuma hanyar da Sin ta zaba wajen raya kasarta. Dadin dadawa, Sin na fatan Amurka na nuna adalci da daidaici kan batun hakkin Bil Adam a kasar Sin. Kuma, Sin ta bukaci Amurka da ta taka rawa wajen raya sabuwar dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare da mutunta juna tare da kawo moriyar juna.
A nata bangare, Amurka ta darajanta ci gaban da Sin ta samu a fannin hakkin Bil Adama, kuma tana fatan kara yin musayar ra'ayi da kasar Sin ta wannan shawarwari. Amurka kuma na fatan kara hada kai da kasar Sin domin kokarin daidaita bambancin ra'ayi dake tsakaninsu, kara amincewa da juna da kuma zurfafa hadin kai.(Amina)