in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakiliyar musamman ta shugaban kasar Amurka Hillary Clinton ta iso birnin Beijing
2012-05-02 14:58:27 cri
A ranar 2 ga wata na safe, wakiliyar musamman ta shugaban kasar Amurka kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta iso birnin Beijing. Haka kuma, a wannan rana da yamma, an bayyana cewa, wakilin musamman na shugaban kasar kuma ministan kudi na kasar Timothy Geithner da sauran wakilan kasar Amurka sun iso birnin Beijing don halartar shawarwari a karo na 4 game da manyan tsare-tsare da tattalin arziki da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka.

Daga ranar 3 zuwa ranar 4 ga wannan wata, za a shirya shawarwari a karo na 4 bisa manyan tsare-tsare da tattalin arziki da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka a nan birnin Beijing, kuma wakilin musamman na shugaban kasar Sin kuma mataimakin firaministan kasar Wang Qishan da mamban majalisar gudanarwa ta kasar Dai Bingguo za su jagoranci shawarwari tare da Madam Clinton da Mista Geithner, haka kuma za su yi shawarwari bisa manyan tsare-tsare da tattalin arziki. Bisa labarin da aka samu, an ce, manyan jami'an hukumomin kasashen biyu sama da 20 za su halarci wadannan shawarwari.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China