A ran 6 ga wata, kwamandan sojojin Amurka na yankin tekun Pacific Samuel Locke Montreal ya amince da matakin da Sin ta dauka na gina babban jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen saman yaki, kuma a ganinsa, sojojin kasashen Sin da na Amurka na dada inganta karfinsu ta fuskar yin shawarwari, yana mai fatan ci gaba da samun bunkasuwa a wannan fanni.
Samuel Locke Montreal ya yi wannan furuci ne yayin taron manema labarun da aka yi a wannan rana a ginin hukumar tsaron kasar Amurka. An ce, a karshen watan Yuni na wannan shekara, Samuel Locke Montreal ya taba kaiwa wata ziyara kasar Sin ta tsawon kwanaki hudu, ziyarar ta zamo karo na farko da wani kwamandan sojojin Amurka a yankin tekun Pacific ya kai wa kasar Sin a cikin shekaru hudu da suka gabata.
Yayin da aka tabo maganar babban jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen saman yaki da Sin ta gina kuwa, Montreal ya amince da wannan matakin da Sin ta dauka, a cewar sa a matsayin ta na kasa da ke cikin sahun gaba a fannin tattalin arziki, Sin na da ikon gina wannan nau'in jirgin ruwa, bisa la'akari da bukatun tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar dama na dukannin duniya.
Bugu da kari, ya ce, Sojojin Amurka za su yi hadin gwiwa da kasar Sin domin ba da tabbaci ga amfanin babban jirgin ruwan yaki na kasar Sin, ta yadda zai tallafa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya. (Amina)