in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin zurfafa hadin kai dake tsakanin kasashen Sin da Amurka
2011-08-02 16:55:07 cri

Ranar Litinin 1 ga wata a birnin Washington,Jakadan kasar Amurka a Kasar Sin Lou Jiahui ya yi ratsuwar kama aiki a karo na farko da zai rike wannan mukami a matsayinsa na dan asalin Kasar Sin.A lokacin ratsarwar ya yi alkawarin cewa, bayan ya kama, zai yi kokarin zurfafa dangantakar hadin kai dake tsakanin kasashen biyu.

A gun bikin, Luo Jiahui ya jaddada cewa, kasashen biyu na da dangantaka mai muhimmanci kuma mai yamutsatse a fannin diplomasiyya, tattalin arziki da tsare-tsare. Bangarorin biyu na fuskantar kalubaloli da makoma mai kyau ta fuskar hadin kai gaba daya. Zurfafa hadin kai ba ma kawai zai kawo babban tasiri ga kasashen biyu ba, har ma yana da babban muhimmanci ga kasashen duniya.

Luo Jiahui ya ce, game da kalubaloli da bambancin ra'ayi dake tsakanin kasashen biyu, yana kokarin neman wata hanyar yin mu'ammala domin isar da matsayin gwamnatin kasar Amurka tare da yin musayar ra'ayi tare da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Sin. A sa'i daya kuma, zai yi kokarin yin mu'ammala tare da jama'ar kasar Sin domin tabbatar da karfafa fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen biyu.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China