in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasar Amurka ta kulla huldar hadin gwiwa mai inganci tare da kasar Sin, in ji mataimakin ministan tsaron kasar Amurka
2012-10-04 17:09:40 cri
Ashton Carter, mataimakin ministan tsaron kasar Amurka ya fadi cewa, wani muhimmin kashi da ke cikin manufar kasar Amurka a fannin sake samun daidaito a yankunan Asiya da tekun Pacific shi ne kulla huldar hadin gwiwa mai inganci tare da kasar Sin.

Mr. Carter ya fadi haka ne jiya Laraba 3 ga wata a lokacin wani taron kara wa juna sani ta fuskar soja da kasar Sin ta shirya a cibiyar masana ta Woodrow Wilson da ke birnin Washington D.C..

Carter ya yi bayanin cewa, kasar Amurka ta tsara manufarta wajen sake samun daidaito a yankunan Asiya da tekun Pacific ne domin tabbatar da zaman lafiya a wannan shiyya a maimakon domin wata kasa ko wata kungiyar da ta samu halartar wasu kasashe, ta yadda dukkan kasashen da ke shiyyar za su samu alheri daga wajen tsaro, kana da kara samun wadata.

Dangane da batun ziyarar da ministan tsaron kasar Amurka Leon Panetta ya kawo wa kasar Sin kwanakin baya, Carter ya ce, hakan yana cikin aniyar kulla huldar hadin gwiwa mai inganci a tsakanin Amurka da Sin wanda wani muhimmin kashi ne da ba a iya rabawa domin tabbatar da samun zaman lafiya da wadata a duk duniya a karni na 21. Wani babban makasudin da ya sa Amurka ta tsara manufar sake samun daidaito a yankunan Asiya da tekun Pacific shi ne kafa wata kyakkyawar dangantakar tsaro mai dorewa a tsakanin Amurka da Sin a fili yadda ya kamata.

Yanzu haka in ji shi, Amurka na neman hadin kai tare da Sin a kan al'amura a jere da suka shafi diplomasiyya, tattalin arziki da kuma tsaro, ciki har da kokarta aza harsashi ga samun dauwamammen ci gaban dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta fuskar soja.

Hakazakila, Carter ya sake jaddada cewa, kasar Amurka ba ta dauki matsayi kan rikicin yankunan kasa da ke tsakanin wasu kasashen da ke yankunan Asiya da tekun Pacific ba, amma za ta ba da tabbaci wajen samun 'yancin tafiye-tafiyen jiragen ruwa da kuma warware rikice-rikice cikin lumana.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China