Wasu mutane 6 da suka hada da maza 2 da mata 4 sun rasa rayukansu, baya ga wasu mutanen 4 da suka samu raunuka, sakamakon wani hadarin mota da ya rutsa da su a kan titin Abuja zuwa Lokoja dake tsakiyar Nigeria a ranar Talatar da ta gabata. Wannan dai hadarin mota ya auku ne a kauyen Karara, bayan da wata karamar motar fasinja ta yi taho-mu-gama da wata karamar safa dake dauke da fasinjoji da dama. Kwamandan rundunar hukumar kare hadurra reshen jihar Kogi Garba Mohammed, ya tabbatar da faruwar wannan lamari, yana mai cewa, tuni aka garzaya da mutane 4 da suka raunana asibiti, yayin da aka kai gawawwakin wadanda suka rasu wajen ajiya dake wani asibiti mallakar jihar.(Saminu)