Yayin ganawa da shugaba Mohammed Morsi wanda ya iso birnin Khartoum a safiyar ranar a ziyarsa ta farko zuwa kasar Sudan bayan hawa kujerar mulki, Al- Bashir ya bayyana cewa suna fatan ganin kasar Masar ta zamo mai muhimmin tasiri a batutuwa da suka shafi yankin da ma duniya, don haka yake neman ganin kasar Masar ta zamo muhimmiya kan batun dangantaka tsakanin Sudan da Sudan ta kudu.
Da yake magana shugaba Morsi ya ce, Masar za ta mara bayan yunkurin kasashen Sudan da Sudan ta kudu wajen warware batutuwa da suke takaddama a kansu domin a cimma zaman lafiya da dorewa, inda ya yi alkwarin ba da dukkan wata gudummawa da za ta inganta tattaunawa tsakanin Khartoum da Juba. (Lami)