Wu Sike ya bayyana ra'ayin da Sin ta dauka game da batun Falesdinu, inda ya yi bayanin cewa, ganin wannan batu ya zama muhimmin batu na Gabas ta tsakiya, kuma yana da tasiri sosai, duk sauyin da za a yi kan halin da ake ciki a shiyyar, ya kamata a mai da hankali game da batun. Ya ce, Sin ta dora muhimmanci sosai game da muhimmiyar rawar da kungiyar AL ta taka game da batun Falesdinu, kuma tana fatan inganta shawarwari da kungiyar, don ci gaba da kokartawa wajen warware batun cikin lokaci.
A nasa bangare kuma, Araby ya yaba wa shugabannin kasar Sin a kan yadda suka dora muhimmanci sosai game da batun Falesdinu, kuma ya ce, kasashen Larabawa sun yi imani cewa, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya game da 'yancin kan kasashen Larabawa, don haka kungiyar AL tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari, don sa kaimi ga yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya.
Har ila yau, a lokacin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna halin da ake ciki a kasar Siriya, kuma suna mai cewa, za su kokarta don ganin yadda za a warware batun Siriya ta hanyar siyasa kuma tun da wuri.(Bako)